IQNA

17:53 - August 05, 2012
Lambar Labari: 2386175

An fara Aiwatar Da Wani Shiri Na wayar Da Kan Mutane Kan Adinin Muslunci A Nahiyar Afirka

Bangaren kasa da kasa, an fara aiwatar da wani shiri na wayar da kan mutane dangane da addinin muslunci a kasashen nahiyar Afirka da nufin tabbatar da cewa an samu kyakyawar fahimta tsakanin musulmin yankunan nahiyar da kuma sauran al’um,momi mabiya wasu addinan na daban da suke cikin nahiyar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya bhabarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo nan a jaridar A-raya, cewa an fara aiwatar da wani shiri na wayar da kan mutane dangane da addinin muslunci a kasashen nahiyar Afirka da nufin tabbatar da cewa an samu kyakyawar fahimta tsakanin musulmin yankunan nahiyar da kuma sauran al’um,momi mabiya wasu addinan na daban da suke cikin nahiyar, kamar dai yadda daya daga cikin mambobin kwamitin zartarwa na majalisar malaman adddinin ta duniya ya sanar.
A wani bangare kuma likitoci a kasar Uganda sun bayyana cewa mai yuwa wasu mutanen da suka kama da cutar nan ta Ebola su tsira da ransu bayan kyautatuwar yanayinsu a cikin jinyan da suke yi. Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto wasu jami’an lafiya a lardin Kibaale na yammacin kasar, inda aka ware mutane 32 wadanda suke fama da wannan cutar ta Ebola. Idan yanayin lafiyarsu ya kara kyautata suna iya sallamarsu nan da yan kwanaki. Ya zuwa yanzu dai mutane 16 suka rasa rayukansu sanadiyyar bullar wannan cutar, wacce bata da magani.
Amma likitoci suna iya magance alamun cutar kamar amai da kuma gudawa. Cutar Ebola dai tana yaduwa ne ta hanyar taba yawu, bayan gida, saduwa da kuma jini na wanda yake dauke da cutar. Mazauna yankina kudancin kasar Uganda dai sun kauracewa garin Kibaale don tsoron kamuwa da cutar. Garin har’ila yau yana kusa da kan iyakar kasar da kasar Congo inda cutar ta fara bayyana a shekara ta 1976. Ministan yawon shakatawa na kasar ta Uganda Ephraim Kamuntu ya bayyana cewa bullar cutar ya gurgunta sana’ar yawon shakatawa a kasar duk da cewa cutar ta shafi lardi guda ne kawai a duk fadin kasar da ke gabcin nahiyar Afirka.
1071285


captcha