Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa a kudu maso yamma na nahiyar Asia cewa, Zainab Bakhsh makaranciyar kur'ani mai tsarki daga jamhuriyar muslunci ta Iran ta halarci gasar karatu da harder kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a kasar Turkiya tare da halartar makaranta mahardata daga sassan na kasar wadanda suke gudanar da karatu domin raya wannan wata mai albarka na azumin watan Ramadan.
A wani rahoton dangane daga kasar ta Iran kuma a taron manema labarai da ya gabatar a yau lahadi, kakakin kwamitin shirya Taron Koli na Kungiyar Kasashen Duinya 'Yan Ba Ruwanmu da za a gudanar daga ranar 26 zuwa 31 ga wannan wata na Agusta a nan Tehran, ya ce Jagoran Juyin juya halin musulunci na Iran ne wato Ayatullahil Uzma Sayyed Ali Khemenei da kuma Babban Magakatarda na Majalisar Dinkin Duniya na daga cikin wadanda za su gabatar da jawabai ga mahalarta wannan taro. Kakakin kwamitin shirya wannan taro Mohammad Reza Forqani ya ce kawo yanzu akwai shuwagabannin kasashe 31 da suka tabbatar da aniyarsu ta halartar wannan taro, wasu kasashe 10 za su turo ministocinsu ne na harkokin waje, sai kuma wasu kasashe 4 da za su turo tawagogi na musamman.
Amma dai sai wasu kasashen da jakadojinsu da ke nan Iran ne za su wakilce su a wannan taro wanda shi ne irinsa na karo na 16 da za a gudanar. Ita dai wannan kungiya ta 'yan ba ruwanmu an kafata ne a shekara ta 1961 a kasar Yougoslavia, kuma a halin yanzu tana da kasashe mambobi 120 da kuma wasu kasashe 21 da ke a matsayin 'yan kallo, kuma babbar manufarta ita ce samar da ci gaba, tsaro da kuma tattalin arziki a tsakanin kasashe mambobinta. A game da taron na Tehran kuwa, shugaban kasar Rasha Vladamir Putin da kuma takwaransa na Turkiyya Abdullah Gul ne aka gayyata a matsayin manyan baki. A taron.
1070851