Kamfanin dilalncin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren yada labaransa na yankin gabas ta tsakiya, cewa sakamakon gagarumar gudunmawar da kamfanin dillanncin labaran iqna ya bayar wajen daukar hotuna da bayar da labarai cikin sauri kan gasar karatu da ahardar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da aka gudanar a birnin Dubai fadar kasuwancin kasar hadaddiyar daular larabawa an bayar da kyutar giramawa gare shi saboda kokarin da ya yi, kamar yadda masu shirya gasar suka sanar.
A wani labarin kuma jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bada labarin shirya zaman tattaunawa kan matsalar Siriya domin warware rikicin kasar ta hanyar lumana. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran a bangaren alaka da kasashen Larabawa da nahiyar Afirika Husaini Amir Ilahiyon a yau litinin ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran zata karbi bakoncin kasashen da suke adawa da duk wani shirin daukan matakin soji kan kasar Siriya, kuma suke bibiyar hakikanin abin da ke faruwa a kasar ta Siriya, don gabatar da shawarwari kan hanyar warware rikicin kasar ta hanyar lumana.
Amir Ilahiyon ya kara da cewa: zaman tattaunawan da za a gudanar a ranar alhamis 9 ga wannan wata na Ogusta zai samu halattan ministocin harkokin wajen kasashe fiye da goma. Har ila yau Ilahiyon ya jadada cewa shirin wanzar da zaman lafiya da Kofi Annan ya gabatar shi ne hanya daya tilo da zata kawo karshen rikicin da kasar Siriya ta afka, don haka zaman tattaunawan na birnin Tehran zai karfafa shirin na Kofi Annan na shiga tsakani.
1072901