IQNA

Taron Kungiyoyin Kare Hakkin Bil Adama A Kasar Tunisia Ya Goyi Bayan Boren Al’ummar Bahrain

11:04 - August 07, 2012
Lambar Labari: 2387479
Bagaren kasa da kasa, taron da kungioyin kare hakkin bil adama na kasashen duniya suka gudanar a birnin Tunis na kasar Tunisia suka gudanar wanda ya kawo karshe a jiya ya fitar da bayaninsa na bayan taro da ke tabbatr da cikakken goyon bayansa ga boren da al’ummar kasar Bahrain suke yi domin neman sauyi ta hanyar lumana.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Iba, cewa zaman taron da kungioyin kare hakkin bil adama na kasashen duniya suka gudanar a birnin Tunis na kasar Tunisia suka gudanar wanda ya kawo karshe a jiya ya fitar da bayaninsa na bayan taro da ke tabbatr da cikakken goyon bayansa ga boren da al’ummar kasar Bahrain suke yi domin neman sauyi ta hanyar lumana, wanda kuma mahukuntan kasar suke yin amfani da karfin tuwo domin murkushe su, kamar dai yadda duniya take shedawa.
Rahotanni daga kasar ta Bahrain sun habarta cewa, jami'an tsaron kasar sun afka kan yankuna da dama domin murkushe fararen hula masu neman sauyi na siyasa a kasar ta hanayar lumana. Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaron na kasar Bahrain sun kai hari a kan yankuna da garuruwa 19 a cikin daren jiya, inda suka yi ta harba hayaki mai sanya hawaye mai dauke da sanadaran guba, gami da harsasan chozen da aka haramta yin amafani da su a bisa dukkanin dokoki na duniya.
Wasu rahotanni da jaridar New York Times ta buga sun tabbatar da cewa, yanzu haka sojojin Amurka 240 sun kammala shiri domin isa kasar Bahrain, da nufin kare masarautar kasar daga boren al'umma, da kuma taimaka ma jami'an tsaro wajen murkushe masu zanga-zangar lumana.
1072420
captcha