Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa ranar qods ta wannan shekara ta zo ne daidai da lokacin da ake sheda fadakar musulmi akasashe da dama musamman na larabawa wanda hakan ya yi sanadiyar kawo karshen mulkin wasu daga manyan masu yi ma yahudawan sahyuniya hidima a yankin kamar yadda ta faru a Masar.
sojin haramtacciyar kasar Isra’ila na cikin yin shirin fuskantar masu zanga-zangar lumana domin ranar kasa inda za su tuna da masallacin Quds ami alfarma da kuma yin kira da a kawo ma al’ummar palastine dauki daga zalunci da suke fama da shi da yahudawan sahyuniya da suka mamaye musu kasa da yankuna, a zirin gaza da kuma gabar yamma da kogin Jordan.
Bayanin ya ci gaba da cewa dubban daruruwan palaesyinawa v acikin yankunan gabar yamma da kogin Jordan da kuma zirin Gaza suke cikin gudanar da zanga-zangar ranar kasa, domin nuna duniya cewa batun palastinu yana raye, a hankoron da wasu daga cikin munafukan kasashen larabawa suke yi na mayar da maganarsu a bun mantawa baki daya a cikin duniyar larabawa da ma duniya baki daya.
Yanzu haka sojin haramtacciyar kasar Isra’ila na cikin yin shirin fuskantar masu zanga-zangar lumana domin ranar kasa inda za su tuna da masallacin Qods ami alfarma da kuma yin kira da a kawo ma al’ummar palastine dauki daga zalunci da suke fama da shi da yahudawan sahyuniya masu tsananin zalunci da danniya.
1076485