IQNA

Shugaban masar Ya Halarci Taron Girmama wadanda Suka Nuna Kwazo A Gasar Kur’ani

22:50 - August 12, 2012
Lambar Labari: 2391258
Bnagaren kasa da kasa, shugaban kasar ya halarci taron da aka gudanar na girmama wadanda suka nuna kwazo a gasar karatun kur’ani mai tsarki gami da harda da aka gudanar a kasar a matsayi na duniya duk kuwa da cewa gasar ba ta kai yadda aka saba gudanar da ita ba saboda yanayin da kasar ta Masar take ciki.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi, cewa shugaban kasar ya halarci taron da aka gudanar na girmama wadanda suka nuna kwazo a gasar karatun kur’ani mai tsarki gami da harda da aka gudanar a kasar a matsayi na duniya duk kuwa da cewa gasar ba ta kai yadda aka saba gudanar da ita ba saboda yanayin da kasar ta Masar take ciki na rashin tsaro, da kuma rashin farfadowa daga abubuwan da ta sheda a tsawon wannan lokaci.
A wani labarin na daban kuma majiyoyin tsaro a kasar Masar sun habarta cewa, a safiyar yau wasu 'yan bindiga sun bude wuta a kan jami'an tsaron kasar da ke yankin Sina'a da ke kan iyakar kasar da yankunan Palastinu da yahudawan sahyuniya suka mamaye. Majiyar ta sheda cewa an kai harin a yankin Ummu Shaihan da ke tsakiyar Sina'a, amma babu wanda ya rasa ransa, wannan hari na yau dai ya zo ne a kwanaki bakwai daiadi da kai wani makamancinsa, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojojin kasar ta Masar 16 da suke gudanar da ayyukan tsaron iyakokin kasar.
Gwamnatin kasar Masar dai ta dora alhakin wadannan hare-hare a kan wasu gungun 'yan salafiyya masu tsatsauran ra'ayi da suke dauke da makamai, ta kuma sha alwashin shiga kafar wando daya su domin murkushe su. Jaridar New York Times ta kasar Amurka ta buga wani rahoto a jiya da ke cewa, gwamnatin Amurka ta yi wa gwamnatin Masar ta yi domin gudanar da ayyukan tsaro na hadin gwiwa tsakaninta da gwamnatin Masar a yankin na Sina, domin tabbatar da tsaro ga iyakokin haramtacciyar kasar Isra'ila.
1076517


captcha