Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na 20min, cewa jami’an tsaron kasar Amurka sun sanar da kai harin ta’addanci kan wani masallaci mallakin mabiya addinin muslunci a cikin jahar Ilinuwa a wani mataki da ake kallon cewa na karuwar kyamar addinin muslunci da mabiyansa ne a cikin kasar da ke raya kare hakkokin bil adam da girmama ra’ayoyi da akidu na sauran mutane da addinansu.
A bangare guda kuma fitaccen malamin addinin musluncin nan na kasar Tunisia Tijani Samawi ya bayyana cewa Imam Shahid Bakir Sadr shi ne mutum na farko a cikin larabawa da ya fara fitar da tunain mikewar al’ummar larabawa domin kalubalantar azzaluman shugabanninsu da kuma muggan sarakuna da suke mulkar al’umma bisa tsari na zalunci da danniya.
Malamin ya bayyana hakan a wagaban wani babban taro da aka kira na tunawa da ranar shahadar Imam bakir Sadr a birnin Najaf mai alfarma, wanda ya samu halartar masana daga sassa daban-daban na duniyar musulmi da ma kasashen Asia da dama, gami da manyan malaman addini da na jami’oi na kasar Iraki, inda ya bayyana siffofinsa da cewa mutum ne da ya sadaukantar da ransa saboda Allah da kuma daukakar addinin Allah.
malamin addinin musluncin nan na kasar Tunisia Tijani Samawi ya bayyana cewa Imam Shahid Bakir Sadr baya ga cewa shi ne mutum na farko a cikin larabawa da ya fara fitar da tunain mikewar al’ummar larabawa domin kalubalantar azzaluman shugabanninsu, shi ne kuma mutumin da ya kalubaanci zalunci dawagitan Iraki.
1077366