IQNA

22:42 - August 16, 2012
Lambar Labari: 2394564

Marzuki Ya Ce Zainul Abidin Ya Yi Wa Musulmin Tunis Ha’inci A Lokacin Mulkinsa

Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Tunisia ya bayyana tsohon shugaban kasar da cewa ya yi ha’inci ga muslunci da kuma al’ummar kasa a lokacin da yake yin suka kan yadda gidan sarautar Ali-saud ya ba shi cikakkiyar kariya bayan da al’ummar kasar suka kawar da shi daga kan karagar mulki.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Megrib, cewa shugaban kasar Tunisia ya bayyana tsohon shugaban kasar da cewa ya yi ha’inci ga muslunci da kuma al’ummar kasa a lokacin da yake yin suka kan yadda gidan sarautar Ali-saud ya ba shi cikakkiyar kariya bayan da al’ummar kasar suka kawar da shi daga kan karagar mulki wanda ya kwashe shekaru ashirin da uku yana kanta.
Yanzu haka an bude wani babban masallaci na kabilar Tatariyawa a Alashar da ke cikin gundumar Azmir wanda taron bde shi ya gudana aranar Alhamis da ta gabata tare da halartar manyan malamai da kuma wasu daga cikin jami’an gwamnatin kasar ta Turkiya.
Wani labarin kuma yana cewa kungiyar kare hakkokin bil adama Amnesty International ta duniya ta yi kaakusar suka cin zarafin dan adam da haramtacciyar kasar Isra’ila take yi a cikin yankunan palastinawa wanda hakan ya yi hannun riga da dukaknin dokoki na kasa da kasa baki daya, tare da neman a kawo karshen zaluncin da suke fuskanta.
Sojin haramtacciyar kasar Isra’ila na cikin yin shirin fuskantar masu zanga-zangar lumana domin ranar kasa inda za su tuna da masallacin Quds ami alfarma da kuma yin kira da a kawo ma al’ummar palastine dauki daga zalunci da suke fama da shi da yahudawan sahyuniya da suka mamaye musu kasa da yankuna, a zirin gaza da kuma gabar yamma da kogin Jordan.
Bayanin ya ci gaba da cewa dubban daruruwan palaesyinawa v acikin yankunan gabar yamma da kogin Jordan da kuma zirin Gaza suke cikin gudanar da zanga-zangar ranar kasa, domin nuna duniya cewa batun palastinu yana raye, a hankoron da wasu daga cikin munafukan kasashen larabawa suke yi na mayar da maganarsu a bun mantawa baki daya a cikin duniyar larabawa.
1079271















captcha