Kmafanin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa a karon farko tashar talabijin din kur’an ta watsa shirinta daga hubbaren Imam Hussain (AS) da ke birnin Karbala mai alfarma a kasar Iraki kai tsaye wanda hakan ya zama daya daga cikin muhimman ayyuakan da wannan tasha ta gudanar tun daga lokacin da aka kafa a hukumar talabijin da radio ta jamhuriyar muslunci.
Ana shirin gudanar da wata gasa kan muhimman abubuwan da addinin muslunci ya ginu a kansu wadda ta kebanci matasa mabiya addinin muslunci na kasar wadda za ta gudana a birnin Rayazan na kasar tare da halartar malaman addini da kuma masana da shugabannin cibiyoyi.
Bayanin ya ce an bude wani masallaci a cikin bababr hedikwatar ‘yan sanda da ke birnin Bankok fadar mulkin kasar Thailand a wani mataki na kara tabbatar da mabiya addnin muslunci da ke kasar a matsayin daya daga cikin mabiya addinai sannu a kasar wadda akasarin mabiya addinain buda.
1080010