Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa an wayi gari a birnin New York na kasar Amurka an lika wasu takardu an nuna kyama ga haramtacciyar kasar Isra’ila da kuma ayyukan ta’addancin da take yi kan al’ummar palastinu marassa kariya wanda musulmin duniya suka kawar da kansu daga hakan musamman kawayen Amurka na yankin da suke raya cewa su ne shugabannin musulmi da suke kiran taruka da sunan musulmi suna aiwatr da manufofin Amurka na siyasa.
Tafiyar da Ali Juma’a ya yi zuwa birnin Qods ya yi ne tare da hadin gwiwa da ma’aikatar tsaro ta haramatcciyar kasar Isra’ila wanda kuma ko shakka babu hakan ya sanya gagarumin shakku a cikin zukatan mutanen kasar dangane da wannan ziyara tasa, duk kuwa da cewa daga cikin abubuwan da ya yi har da duba lafiyarsa a asibiti.
Yan majasar dokokin kasar Masar sun yi kira da a safke babban malamin kasar mai bayar da fatawa bayan ya yi tafiya zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da izinin majalisa da kuma yin shawara da majalisar malaman addinin muslunci ta kasar ba duk kuwa da cewa bisa doka sai sun amince masa. 1079852