IQNA

17:37 - August 17, 2012
Lambar Labari: 2394997

Ya kamata Shugabannin Kasashen Musulmi Su Dauki Mataki Kan Batun Qods

Bangaren kasa da kasa, kungiyar hamas da ke iko da yankin Gaza ta kirayi shugabannin kasashen msuulmi da suke gudanar da taruka abirnin Makka da su dauki matakan da suka dace kan batun ta’annutin haramtacciyar kasar Isra’ila da yahudawa masu tsatsauran ra’ayi kan masallacin Qods da kuma wurare masu alfarma da ke birnin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palstine Info cewa, kungiyar hamas da ke iko da yankin Gaza ta kirayi shugabannin kasashen msuulmi da suke gudanar da taruka abirnin Makka da su dauki matakan da suka dace kan batun ta’annutin haramtacciyar kasar Isra’ila da yahudawa masu tsatsauran ra’ayi kan masallacin Qods da kuma wurare masu alfarma da ke birnin na Qods alkiblar musulmi ta farko.
Hankoron da haramtaccioyar kasar Isara’ila take na ganin cewa ta mamaye birnin Qods da dukaknin kaddarorin musulmi da mabiya addinin kirista da suke cikin wannan birnin mai alfara na daga cikin alamun da suyke nuni da kawo karshen haramtacciyar kasar yahudawan sahyuniya wadda ta zama bababr sankara ga al’ummomin duniya.
A bangare guda kuma an gudanar da wani zaman taro a birnin Gaza domin yin kira ga dukaknin al’ummomin musulmi da na larabawa da su mike domin kwato masallacin Qods mai alfarma daga mamayar yahudawan sahyuniya, duk kuwa da cewa shekara da shekaru ana yin wannan kira amma da sannu ya fara tasiri a cikin zukatan musulmi da larabawa da sauran al’ummomi masu lamiri.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro ya samu halartar masana da malaman addinin muslunci daga sassa daban-daban na yankunan da ke cikin zirin Gaza, kamar yadda wasu daga cikin mahalartan suka gabatar da laccoci da makaloli dangane da halin da ake ciki a birnin Qods, inda dukaknin wurare masu alfarma da ke birnin da kewaye ke fuskantar barazanar rushewa daga yahudawan sahyuniya, da hakan ya hada da masallaci mai albarka.
Masana da malamai sun gudanar da wani zaman taro a birnin Gaza domin yin kira ga dukaknin al’ummomin musulmi da na larabawa da su mike domin kwato masallacin Qods mai alfarma daga mamayar yahudawan sahyuniya, domin kara fito da matsayin wannan birnin mai albarka a wajen mabiya addinin muslunci da kiristanci na duniya baki daya.
1079687













captcha