Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin Almanar cewa, a yau shugaban kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah zai yi magana kan batun Qods da kuma gwagwarmayar palastinawa a jawabin da zai gabatar kan ranar Qods da kuma muhimmancin da take da shi ga al’ummar musulmi da kuma abin da za aiya koyo daga darussan wannan rana mai albarka da ake raya batun Qods a dukaknin kasashen duniya.
Babban sakataren kungiyar hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa duk da matsin lamaba daga manyan kasashen duniya da jamhuriyart mslunci ta Iran take fuskanta saboda goyon bayan da take baiwa al’ummar palastinu amma wannan bai sanya ta rabu da batun ba domin magana ce ta makoma ga musulmi da kimar addininsu domin kuwa ba batu ne na siyasa ba.
Sakataren kungiyar gwagwarmayar musulunci a kasar Lebanan Sayyid Hassan nasrullah ya jadadda goyon bayansa ga jagoran juyin juya halin muslunci da kuma shugaban jamhuriyar musulunci ta Iran kan gagarumar gudunmawar da suke bayarwa adukaknin bangarori na ci gaba n al’ummar musulmi. 1080895