Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Qabs, cewa kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta yi kakakusar da yin Allawadai da keta alfarmar kur’ani mai tsarki da kuma littafin Innjila da haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a wani mataki na cin zarafin addinan muslunci da kuma kiristanci wanda kuma dama bisa ga al’ada haramtacciyar kasar ba ta girmama kowane addini hatta da ma addinin yahudanci na hakika.
Haramtacciyar kasar Isra’ila ce take amfana da salon siyasar dabbanci da wawanci da wuce gona da iri ta mabiya tafarkin salafiyya da suke cikin gwamnatin kasar Masar a halin yanzu inda suke bata sunan muslunci da bakanta fuskarsa da siyasara mai tsarki a idon duniya kamar yadda kowa ya gani a cikin ‘yan watanni da suka yi mulki.
A kasar Jamus kuwa ministan harkokin cikin gidan kasar ne ya yi kakkausar suka kan mabiya tafarkin salafiyya dangane da abubuwan da suke yi a kasdar na wuce gona da iri da sunan cewa suna bin tafarkin addinin mulsunci ne da kuma rarraba kur’anai a tsakanin al’ummar kasar ta Jamus.
A bangare guda kuma ana shirin gudanar da wani shiri na musamman dangane da bayar da horo ga limaman masallatai na kasar Jamus, wanda jami’ar Snaburg ta kasar za ta dauki nauyin aiwatar da shi tare da hadin gwai da cibiyoyin mabiya addinin muslunci na kasar baki daya, wanda kuma ake ganin zai amfani matuka.
1080816