IQNA

23:05 - August 18, 2012
Lambar Labari: 2395904

A Karon Farko Shugaban Kasar Masar Zai Ziyarci Jamhuriyar Muslunci Ta Iran

Bangaren kasa da kasa, a karon farko shugaban kasar Masar zai ziyarci jamhuriyar muslunci ta Iran tun bayan samun nasarar juyin juya hali kamar dai yadda ofishin da ke kula da shirya taron kasashen yan ba ruwanmu ya fada a cikin wannan mako da ake shirin fara gudanar da tarukan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa a karon farko shugaban kasar Masar zai ziyarci jamhuriyar muslunci ta Iran tun bayan samun nasarar juyin juya hali kamar dai yadda ofishin da ke kula da shirya taron kasashen yan ba ruwanmu ya fada a cikin wannan mako da ake shirin fara gudanar da tarukan a matsayin ministocin harkokin waje zuwa ga shugabannin kasashe.
Bangare guda kuma wani rahoton yana cewa ana shirin gudanar da wani baje koli na kayan abinci na halal a birnin paris na kasar faransa tare da hadin gwiwa da cibiyoyin mabiya addinin muslunci wadanda suke da dangantaka da kamfanonin kasar da suke samar da ababen bukata bisa yarjejeniya a tsakaninsu da wadannankamfanoni, inda a halin yanzu za su kawo kaya na ahalal bisa yarjejeniyar.
Baje kolin zai nuna irin kayan da ake samarwa a kasashen muslmi da suke samar da kayan abincin halal kuma suke fitar da su zuwa kasashen ketare, daga ciki kuwa har da kamfanonin kasashen malazia da Indonesia gami da wasu daga cikin kasashen musulmi da na larabawa, baje kolin zai taimaka matuka wajen banbance kayayyakin a tsakanin sauran kayan abinci da ake sayarwa a shaguda da kwasunnin kasar.
Gudanar da wannan baje koli na kayan abinci na halal a birnin paris na kasar faransa tare da hadin gwiwa da cibiyoyin mabiya addinin muslunci wadanda suke da dangantaka da kamfanonin kasar da suke samar da ababen bukata bisa yarjejeniya a tsakaninsu yana da matukar muhimmanci ga mabiya addinin muslunci da suke zaune a kasar wadda ba ta musulmi ba.
1080744












captcha