Kamfanin dilalncin labaran iqnaya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tahar talabijin din Al-alam, cewa jami’an tsaron sarki Bahrain sun kai hari kan masu gudanar da janazar daya daga cikin wadanda suka yi shahada a lokacin da suke gudanar da jerin gwanon ranar Qods a ranar juma’ar da ta gabata kamar dai yadda dukaknin rahotanni suka tabbar faruwar hakan a wannan rana.
Gwamnatin HKI ta damu da yadda gwamnatin kasar Masar take shigo da manya manyan makamai a yankin Sina a kokarin da take na fuskantar yan ta’adda dauke da makamai a yankin.
Wani jami’in gwamnatin HKI ya bayyana a ranar litinin da ta gabata cewa gwamnatin Natanyahu ta na son a warware batun ta hanyar shiga tsakani daga bangaren Amurka ko kuma wata kasa daga ciki n kasashen yamma.
Jami’in ya kara da cewa jigilar makamai wanda gwamnatin kasar Masar take yi zuwa yankin sina ya sabawa yerjejniyar Camp Devid ta shekara 1979.
Yerjejjeniyar dai ta takaidawa gwamnatin kasar Masar kai kawo da makamai a yankin Hamadar Sina sai tare da amincewar HKI. Amma tun bayan juyin juya halin da da kauda Husane Mubarak daga kujerar shugabancin kasar masar da kuma dora Muhammad Mursi kan kujerer dangantaka tsakanin makobtan yake kara tabarbarewa.
Gidajen television na kasar masar dai sun nuna babban komandan sojojin kasar kuma ministan tsaron kasar General Abdel Fattah al-Sisi yana jawabi wa sojojin kasar a yankin na sinaa a bayansa kuma akwai jerin tankunan yaki wadanda gwamnati ta kawo don yakar yan ta’adda wadanda ake ganin HKI kanta ce ta samar da su.
1082962