IQNA

22:50 - August 22, 2012
Lambar Labari: 2397249

Shekaru 43 Da Yahudawan sahyuniya Suka Kone Masallacin Qods Mai Alfarma

Bangaren kasa da kasa, shekaru arba’in da uku kenan da yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra’ayi suka kone masallacin Qods mai alfarma tare da taimakon gwamnatocin kasashen yammacin turai musamman manyan munafukai daga cikinsu Amurka da Birtaniya wadanda su ne sukakafa haramtacciyar kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam, cewa shekaru arba’in da uku kenan da yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra’ayi suka kone masallacin Qods mai alfarma tare da taimakon gwamnatocin kasashen yammacin turai musamman manyan munafukai daga cikinsu Amurka da Birtaniya wadanda su ne sukakafa haramtacciyar kasar ta yahudawan sahyuniya.
A nata bangaren kungiyar palastinawa ta Hamas ta wata barazana da ke cewa ba za ta taba daina kalubalantar yahudawan sahyuniya kan batun masallacin Qods mai alfarma ba kuma ba za ta taba barin yahudawan su ci gaba da keta alfarmar wannan wuri mai tsarki ba kamar yadda ba ta yi hakan a baya ba.
Ita kuwa kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta fitar da wani bayani dangane da tunawa da zagayowar shekraru arba’in da uku da yahudawan sahyuniya suka kone masallacin Qods mai alfarma duk kuwa da cewa babu wani aiki da aka gani daga kungiyar na kalubalantar abin da haramtacciyar kasar yahudawan sahyuniya take aikatawa kan musulmi da ma larabawan palastinu.
1083240
captcha