IQNA

Tashar talabijin Din Alkausar tan Gudanar Da wani Shiri Domin Fallasa Fina-Finan Turai

22:49 - August 22, 2012
Lambar Labari: 2397250
Bangaren kasa da kasa, gidan talabijin Al-kausar da ke watsa shirinsa kai tsaye a kan tauraron dan adam daga birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci ya fara gudanar da wani shiri na tattaunawa kan fina-finan kamfanin Holywood da kuma fallasa makircin da ke tattare a ciknsu da illarsu ga sauran al’ummomin duniya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizona banagren yada labarai na tashar talabijin din Alkausar, cewa gidan talabijin Al-kausar da ke watsa shirinsa kai tsaye a kan tauraron dan adam daga birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci ya fara gudanar da wani shiri na tattaunawa kan fina-finan kamfanin Holywood da kuma fallasa makircin da ke tattare a ciknsu da illarsu ga sauran al’ummomin duniya musamman ma musulmi daga cikinsu.
Daya daga cikin jagororin masu adawa da salon mulkin kama karya na kasar Bahrain ya bayyana cewa jami’an tsaron kasar tare da ‘yan bangar masarautar kasar suna ci gab ada kai farmaki kan gidajen wadanda suke jagorantar zanga-zangar neman sauyi a fadin kasar da hakan ya hada birnin Manama, da ma wasu sauran yankuna.
Wani labarin kuma ya ce limamin juma'a a nan birnin Tehran, ya ce kisan da makiya ke yi wa malaman kimiya na kasar, ba abin da zai cusa wa al'ummar kasar face farkawa da kuma kare martabobin kasar a kowadanne fagage na rayuwa, musamman wannan bangare na ilimimin nukiliya da Iran take ggudanar da ayyukanta a cikin na zaman lafiya domin amfanin fararen hula.
A lokacin da yake gabatar da hudubar sallar juma'a a masallacin jami'ar Tehran a yau, Ayatullahi Mohammad Emami-Kashani, ya ce kisan na baya-bayan nan da makiya suka yi wa malamin kimiyyar nukiliya na kasar mai suna Mustafa Ahmadi Roshan, wata alama ce da ke kara nuna wa duniya irin damuwar da kasashe da ke hamayya da Iran din ke da ita dangane da irin ci gaba da kuma 'yancin da kasar take da shi na dogoro da kai a fannoni na bincike da kuma kimiya. 1083253

captcha