IQNA

18:01 - August 27, 2012
Lambar Labari: 2400213

Yan Salafiyya Sun Rusa Wasu Daga cikin Wuraren Tarihin Muslunci A kasar

Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin masu bin tafarkin wahabiyanci ko salafiyya sun kai hari kan wasu daga cikin wuraren tarihi da ke cikin kasar Libya da kuma kabrukan waliyai lamarin da yasa sanya ta sanar cewa ba za ta amince da hakan ba kuma za ta dauki matakan ladabtarwa kan wadanda suka yi hakan.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na letemps, cewa, wasu daga cikin masu bin tafarkin wahabiyanci ko salafiyya sun kai hari kan wasu daga cikin wuraren tarihi da ke cikin kasar Libya da kuma kabrukan waliyai lamarin da yasa sanya ta sanar cewa ba za ta amince da hakan ba kuma za ta dauki matakan ladabtarwa kan wadanda suka yi hakan.
A wani labarin kuma gwamnatin Sudan ta tabbatar da dauki ba dadi tsakanin sojojinta da 'yan tawayen kasar a yankin Al-Mouraib da ke arewa maso gabashin lardin Kordofan da Kudu. Kakakin rundunar sojin Sudan Al-Sawarmi Sa'ad Khalid a jiya asabar ya bayyana cewa; Sojojin gwamnatin Sudan sun murkushe 'yan tawayen kasar na kungiyar Sudan People's Liberation Movement-North "SPLM-na Arewaci" a yankin Al-Mouraib da ke arewa maso gabashin lardin Kordofan ta Kudu a wani harin kare kai da ya haifar da gumurzu a tsakanin bangarorin biyu lamarin da ya yi sanadiyyar halaka 'yan tawaye goma sha daya. Sa'ad Khalid ya kara da cewar sojojin gwamnati sun kuma fatattaki 'yan tawayen na SPLM-na Arewaci daga yankunan da suka mamaye na Kershola, Ummul-Baraka, Al-Farsha da El-Oneinat. A nata bangaren kungiyar 'yan tawayen ta SPLM-na Arewaci ta yi da'awar kashe sojojin gwamnati 30 a gumurzun na yankin Al-Mouraib, tare da zargin sojojin gwamnati da kona gidaje da dukiyoyin jama'ar yankin.
Gwamnatin Sudan ta tabbatar da dauki ba dadi tsakanin sojojinta da 'yan tawayen kasar a yankin Al-Mouraib da ke arewa maso gabashin lardin Kordofan da Kudu. Kakakin rundunar sojin Sudan Al-Sawarmi Sa'ad Khalid a jiya asabar ya bayyana cewa; Sojojin gwamnatin Sudan sun murkushe 'yan tawayen kasar na kungiyar Sudan People's Liberation Movement-North "SPLM-na Arewaci" a yankin Al-Mouraib da ke arewa maso gabashin lardin Kordofan ta Kudu a wani harin kare kai da ya haifar da gumurzu a tsakanin bangarorin biyu lamarin da ya yi sanadiyyar halaka 'yan tawaye goma sha daya. Sa'ad Khalid ya kara da cewar sojojin gwamnati sun kuma fatattaki 'yan tawayen na SPLM-na Arewaci daga yankunan da suka mamaye na Kershola, Ummul-Baraka, Al-Farsha da El-Oneinat.
A nata bangaren kungiyar 'yan tawayen ta SPLM-na Arewaci ta yi da'awar kashe sojojin gwamnati 30 a gumurzun na yankin Al-Mouraib, tare da zargin sojojin gwamnati da kona gidaje da dukiyoyin jama'ar yankin.
1085027


captcha