IQNA

Ana Shirin Gudanar da Wata Gasar Karatu Da Hardar Kur’ani mai Tsarki A Birtaniya

18:00 - August 27, 2012
Lambar Labari: 2400214
Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da wata gasar karatun kur’ani mai tsarki a kasar Birtaniya tare da halartar wakilan makarantu da kuma cibiyoyin mabiya addinin muslunci da suke kasar kamar dai yadda bayanin ya tabbatar da hakan a jiya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na start right, cewa ana shirin fara gudanar da wata gasar karatun kur’ani mai tsarki a kasar Birtaniya tare da halartar wakilan makarantu da kuma cibiyoyin mabiya addinin muslunci da suke kasar kamar dai yadda bayanin ya tabbatar da hakan a jiya a babban ofishin cibiyar muslunci da ke birnin London.
A wani labarin kuma na daban ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada aniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta karfafa kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM da manufofinta. A jawabinsa na sharen fagen bude zaman babban taron kasashen kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM karo na 16 a birnin Tehran na kasar Iran a yau lahadi; Ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Akbar Salihi ya bayyana cewa.
Akwai bukatar daukan kwararan matakai daga dukkanin kungiyoyin kasa da kasa kan batun zaman lafiya da sulhu a duniya, tare da fayyace cewar siyasar ta'addanci da barazana tana matsayin ha'inci ne ga Majalisar Dinkin Duniya da aka kafa ta a kan kyawawan manufofi da suka hada kasashen duniya, sakamakon haka batun wanzar da zaman lafiya da aminci sune muhimman al'amuran da za a sanya gaba domin warware matsalolin da suke addabara duniya.
Ali Akbar ya kuma kara da cewar yana daga cikin muhimman harkar difilomasiyyar kasar Iran wajabcin ganin an tafiyar da duniya a kan muhimman batutuwa, tare da rashin kawar da kai daga kan barazanar matsalar tsaro, tattalin arziki da gurbatar yana yi, saboda al'amura ne da suke bukatar samun hadin kan dukkanin duniya domin kawar da su.
Har ila yau Salihi ya tabo batun fuska biyu da sanya siyasa da wasu manyan kasashen duniya ke yi a harkar kare hakkin bil-Adama da amfani da ita a matsayin makami domin sanya matsin lamba kan kasashe, don haka zaman taron kungiyar ta NAM zata yi nazari kansu.
1085186



captcha