IQNA

Za A Gudanar Da Wani Zama Taro Na Mawaka Kan Sace Imam Musa Sadr

22:24 - August 29, 2012
Lambar Labari: 2401563
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taro na tuwa da ranar sace Imam Musa Sadr da tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Libya Mu’ammar Gaddafi ya yi tun kimanin shekaru talatin da biyar da suka gabata wanda kuma har inda yau take babu labari kan makomarsa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Alalam, cewa za a gudanar da wani zaman taro na tuwa da ranar sace Imam Musa Sadr da tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Libya Mu’ammar Gaddafi ya yi tun kimanin shekaru talatin da biyar da suka gabata wanda kuma har inda yau take babu labari kan makomarsa yayin da wasu suke zaton cewa ya yi shahada, wasu kuma suke zaton cewa yana da ransa.
Shugaban majalisar dokokin kasar Lebanion Nabih Birri ya sheda cewar, daya daga muhimmanabubuwa da gwamnatin kasar Lebanon ta mayar da hankali kansu a halin shi ne sanin makomar Imam Musa Sadr a kasar Libya bayan da marigayi kanar Gaddafi ya sace shi tare da abokan tafiyarsa su biyu tun sama da shekaru talatin da hudu da suka gabata.
A bangare guda kuma ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar kasar Lebanon ta Al-intiqad cewa, kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ta yi kakausar suka tare da yin Allawadai da halartar wasu daga cikin kasashen larabawa taron da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta gudanar mai taken tsaron yahudawan sahyuniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa ko shakka babu irin mika wuya da wasu daga cikin larabawa ke yi kai tsaye ga manufofin yahudawan sahyuniya, ya kara tabbatar da cewa dukkanin abin da haramtacciyar kasar Isra’ila take na cin zarafin al’ummar palastinu da sauran larabawa akwai hadin baki tsakaninta da wasu daga mayaudaran gwamnatocin larabawa.
1086758





















captcha