Bangaren siyasa, a lokacin da yake gabatar da jawabin bude zaman taron, jagoran juyin juya halin yay i ishara da muhimmancin da wannn kungiya take da shi a matsayin siiasa ta duniya, da kuma rawar da take takawa a matsayi na kasa da kasa, kasantuwar mambobin kungiyar su ne kashi biyu bisa uku na dukkanin kasashen duniya, inda ya ce za su samar da wani canji da zai daidaita siyasar da duniya take tafiya a kanta ta rashin adalci
Jagoran juyin juya halin Musulunci sayyaed Aliyul Khaminaee ne yake bude taron shuwagabanin kasashen kungiyar ta NAM a halin yanzu a dakin taro na nan hukumar gidajen radio da telivison a nan Tehran.
Bayan jawabin jagoran juyin juya halin Musulunci Aya. Sayyeed Aliyul Khaminaee shugaban kasar masar Muhammad Mursi ne zai gabatar da jawabi na farko a matsayinsa na shugaban kungiyar ta NAM, a cikin jawabin nasa Mursi zai gabatar da rahoton ayyukan kungiyar na tsawon shekarun da kasarsa take shugabancin ta, sannan ya mika jagorancin kungiyar ga shugaban kasar Iran Dr Mahmood Ahamadi Najad. Bayan jawabin Shugaban kasar Iran ne babaan sakataren MDD bankin Moon zai gabatar da jawabinsa.
Kasashe 25 ne suka kafa kungiyar NAM a shekara 1961 a birnin begrade na tsohuwar kasar Yogoslavia, kuma ya zawa yau wannan shi ne taro kungiyar karo na 16. Kuma tana da kasashe 120 a matsayin membobi sai kuma wasu kungiyoyin kasa da kasa kamar MDD da kuma wasu kasashen masu sanya ado ko baki a cikinta kamar kasar Rasha. Kungiyar NAM dai ita ce kungiya mafi girma a duniya bayan MDD.