IQNA

22:44 - September 01, 2012
Lambar Labari: 2402808

Palastinawa Sun Yi Na’am Da Jawabin jagora A taron Kasashen Yan ba Ruwanmu

Bangaren kasa da kasa, palastinawa da dama sun yi na’am da bayanin da jagoran juyin juya halin muslunci na Iran ya yi dangane da makomar al’ummar palastinu da kuma muhimmancin mayar da hankali kan wannan lamari zai taimaka wajen kawo karshjen matsalar da wannan al’umma take ciki tsawon shekaru da dama.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya sheda cewa, shi ma a nasa bangaren firayi ministan kasar Indiya Manmahon Singh wanda shugaban kasar Iran Dakta Mahmud Ahmadinejad ya ke wa jagoranci ya bayyana farin cikinsa mai yawan gaske da samun damar ganawa da Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran.
Har ila yau kuma yayin da ya ke ishara da irin tsawon tarihi da kyakkyawar alaka ta al'adu da ci gaba da ke tsakanin al'ummomin kasashen Iran da Indiya, firayi ministan na Indiya ya ce: kasar Indiya tana fatan ganin alakarta da Iran ta kara bunkasa a bangarori daban-daban ciki kuwa har da fagen makamashi da abubuwan gina kasa.
Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da tattaunawarsu da shugaban kasar Iran ya kara dacewa: a yayin wannan ganawar an cimma wasu yarjejeniyoyi masu kyaun gaske a fagagen karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Har ila yau kuma yayin da ya ke ishara da cewa alaka ta kasa da kasa dai ba abu ne abin dogaro da shi sosai ba, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Daya daga cikin irin wadannan kawaye na kasa da kasa wacce ba za a iya dogaro da ita ba, ita ce kasar Amurka wacce babbar kawa a wajenta kuma abar yarda ita ce gwamnatin yahudawan sahyoniya.
1088764








captcha