IQNA

17:56 - September 02, 2012
Lambar Labari: 2403543
Bangaren kasa da kasa, nan ba da jimawa ba za a bude reshe na bankin muslunci a kasar Jamus domin amfanin musulmin kasar da suke da maukar bukatuwa da shi domin harkokinsu na kudade kamar yadda duykaknin bangarori suke da damar su amfana da shi kamar dai yadda bayanin ya tabbatar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto dag shafin sadarwa na yanar gizo na safirnews, cewa nan ba da jimawa ba za a bude reshe na bankin muslunci a kasar Jamus domin amfanin musulmin kasar da suke da maukar bukatuwa da shi domin harkokinsu na kudade kamar yadda duykaknin bangarori suke da damar su amfana da shi kamar dai yadda bayanin ya tabbatar hakan.
A wani labarin na daban kuma, a zantawarsu ta wayar tarho da Manzon Musamman da Majalisar Dinkin Duniya ke shirin turawa zuwa kasar Siriya Lakhdar Brahimi, ministan harkokin wajen kasar China Yang Jiechi, ya jaddada matsayin kasar ta China kan cewa dole ne a yi amfani da hanyoyi na diplomasiyya wajen warware rikicin kasar Siriya amma ba ta hanyar tursasawa ba.
Har ila yau ministan na harkokin wajen China, ya ce akwai bukatar Lakhdar Brahimi ya mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi ayyukan jinkai, sakamakon yadda yakin da ake gwabzawa a Siriyar ya rutsa da dubban mutane. Shi kuwa Lakhdar Brahimi ya bayyana cewa China kasa ce mai matukar muhimmanci wacce kuma za ta iya taka gagarumar rawa wajen warware wannan rikici na kasar Siriya.
Wadannan kalamai na ministan harkokin wajen kasar China, sun zo ne a daidai lokacin da takwaran aikinsa na kasar Rasha Sergei Lavrov yake cewa ''ba ta yadda kasar Siriya za ta janye sojojinta daga cikin garuruwan da 'yan ta'adda suka kutsa kamar dai yadda kasashen Yamma suka bukata'' yana mai cewa alhaki ya rataya a wuyan gwamnatin Siriya na ta kare kasar da kuma al'ummarta.
1088746


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: