IQNA

Musulmin Jamus Sun Yi Allawadai Da Raba Wasu Takardu Na Kin Musulunci

17:58 - September 05, 2012
Lambar Labari: 2406005
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin Musulunci a kasar Jamus sun nuna rashin jij dadinsu dangane da wata poster da ke cin zarafin musulmi a kasar a wani mataki na tsaokana wanda masu tsananin kiyayya da Musulunci na kasar suke yi tun sama da shekaru biyar da suka gabata.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na press TV, cewa mabiya addinin Musulunci a kasar Jamus sun nuna rashin jij dadinsu dangane da wata poster da ke cin zarafin musulmi a kasar a wani mataki na tsaokana wanda masu tsananin kiyayya da Musulunci na kasar suke yi tun sama da shekaru biyar da suka gabata sakamakon harin sha daya ga watan satunba.
Jami'an tsaron kasar Masar sun yi dauki ba dadi da wasu gangun jama'a da suke goyon bayan 'yan tawayen kasar Siriya a birnin Alkahira a jiya talata. Kamfanin dillancin labaran Reuters ya habarto daga wani jami'in tsaro cewa: A jiya Talata wasu gungun jama'a da suke da'awar kare hakkin bil-Adama sun yi kokarin kutsa kai cikin ofishin jakadancin kasar Siriya da ke birnin Alkahira da nufin daga tutar 'yan tawayen Siriya maimakon na gwamnatin kasar, don haka jami'an 'yan sanda suka taka musu burki, lamarin da ya janyo dauki ba dadi da har ya kai ga samun raunuka a tsakanin bangarorin biyu, tare da kame wasu mutane biyar daga cikin gungun jama'ar.
Tun a cikin watan Maris na shekara ta 2011 ce yunkurin neman aiwatar da gyara a fuskar siyasar kasar Siriya ya kunno kai, amma kasar Amurka da kawayenta na kasashen yamma gami da 'yan koransu na kasashen Larabawa musamman Saudiyya da Qatar da kuma Turkiyya da ke makobtaka da Siriya suka dauki matakin samar da 'yan ta'adda tare da mallaka musu makamai da nufin kawar da gwamnatin Bashar Asad saboda matsayinsa na bijirewa bakar siyasar yammacin Turai da goyon bayan kungiyoyin gwagwarmaya, lamarin da ya wurga kasar ta Siriya cikin rikici da rashin zaman lafiya.
1090528



captcha