IQNA

Musulmin Ingila Sun Nuna Rashin Amincewa Da Canja Tarihin Muslunci

22:16 - September 05, 2012
Lambar Labari: 2406062
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a kasar Birtaniya sun nuna rashin amincewa da wani mataki da gwamnatin kasar dauka na caja tarihin muslunci a cikin wani na talabijin din kasar inda msuulmin suka shigar da kara kan wannan danyen mataki domin cin zarafin musulmi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto dag shafin sadarwa na yanar gizo na come4news, cewa mabiya addinin muslunci a kasar Birtaniya sun nuna rashin amincewa da wani mataki da gwamnatin kasar dauka na caja tarihin muslunci a cikin wani na talabijin din kasar inda msuulmin suka shigar da kara kan wannan danyen mataki domin cin zarafin musulmi da kuma tsookanarsu.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa "Amnesty International "ta bukaci a gudanar da bincike akan kisan da jami'an tsaro su ka yi wa wani mai zanga-zanga a gabacin saudiyya, a wani bayani da kungiyar ta kare hakkin bil'adama ta fitar ta bukaci a yi bincike mai zaman kanshi akan kisan da aka yi wa Isam Muhammad Abu Abdullah a lokacin da ya ke cikin zanga-zanga a garin Awamiyyah da ke gabacin Saudiyya.
Bayanin kungiyar ya ci gaba da cewa: "Zanga-zangar ranar alhamis din da ta gabata an yi ta ne domin kira da a saki fursunonin siyasa da ake tsare da su da kuma kawo karshen wariyar da ake yi wa 'yan shi'a a yankin, a cikin watannin bayan nan dai jami'an tsaron Saudiyya sun rika bude wuta akan masu zanga-zangar lumana da su ke son a samar sa sauye-sauye na siyasa a cikin kasar.
Ana shirin gudanar da babban taro dangane da makomar fadakar musulmi a kasashen larabawa da kuma yadda hakan zai yi tasiri wajen dawo da karamar al’ummomin da suka samu kubuta daga zaluncin sarakuna da shugabanni masu danne hakkokin al’ummomin kasashensu.
1091177




captcha