IQNA

17:50 - September 11, 2012
Lambar Labari: 2409958

Mutanen Bahrain Suna Rayuwa karkashin Zalunci Na Gidan sarautar Al Khalifa

Bangaren kasa da kasa, al’ummar kasar Bahrain su ne al’ummar da suka fi kowace al’umma zama abin zalunta ayankin gabas ta tsakiya baki daya domin kuwa ana zaluntarsu a dukkanin bangarori da ya hada zaluncvi na zahiri da mahukunta key i musu da kuma zalunci na kafofin yada labarai.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-alam, cewa al’ummar kasar Bahrain su ne al’ummar da suka fi kowace al’umma zama abin zalunta ayankin gabas ta tsakiya baki daya domin kuwa ana zaluntarsu a dukkanin bangarori da ya hada zaluncvi na zahiri da mahukunta key i musu da kuma zalunci na kafofin yada labarai na larabawa da na kasashen turai.
Sojojin Syria sun sanar cewa sun samu nasarar hallaka wasu daga cikin jagororin ‘yan ta’addan kasar da suke samun goyon bayan Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila da wasu daga cikin kasashen larabawa.

A wata zantawa da ta hada daya daga cikin kwamandojojin sojin kasar Syria da dan rahoton tashar talabijin din Al-alam daga garin Aleppo, ya tabbatar masa da cewa a jiya juma’a sun kai samame a wasu yankuna a cikin garin Harim da ke kan iyaka da Turkiya, bayan da mutanen garin suka sanar da sojoji cewa daruruwan ‘yan ta’adda dauke da muganna makamai sun taru a wurin, ya ce sojojin gwamnatin Syria sun yi amfani da dabaru na yaki wajen hallaka da dama daga cikin ‘yan ta’adda da suka hada har da wasu jagororinsu da ake nema, an kuma kame wasu daga cikinsu daga suka hada har da wasu wadanda ba ‘yan kasar Syria ne ba suna dauke da muggan makamai.

A jiya ne dai ‘yan ta’addan na Syria suka kai wasu munanan hare-hare a cikin birnin Damascus,inda suka kashe jami’an tsaro da fararen hula, sun kuma tayar da wasu bama-baman a kusa da kofar wani masallacin juma’a da ke yankin Rukn a cikin birnin Damascus, a lokacin da mutane suke fitowa bayan kammala sallar Juma’a, lamarin da a nan ma ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula tare da jikkatar wasu.

1095475













captcha