Kamfanin dilalncin labran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi cewa, dubban musulmi a kasar Masar sun yi wani babban gangami a gaban ofishin jakadancin kasar Amurka da ke birnin Alkahira domin nuna rashin amincewa da kuma yin Allawadai da kakakusar murya kan fitar da wani fim na cin zarafin addinin muslunci da aka shirya akasar Amurka a cikin makon nan.
yau an wayi gari lamarin palastinu shi ne mafi muhimamnci a halin yanzu a cikin dukkanin lamaurra da suka shafi musulmi da kuma larabawa baki daya amma makiya musulunci suna ci gaba yin kokarin ganin sun kawar da hankulan al’uimmomin kan lamarin palastinu da kuma zaluncin da suke fuskanta daga yahudwan sahyuniya da ‘yan korensu.
A nasa bangaren babban hafsan hafsoshin sojojin Iran Janar Husain Firouz'abadi ya ja kunnen HKI da cewa za ta fuskantar mummunar mayar da martani sannan kuma mai ruguzarwa daga wajen Iran matukar dai gigi ya debe ta ta kawo mata hari.
Babban hafsan sojojin na Iran ya bayyana hakan a wata ganawa da ya yi da manyan jami'ai da kwamandojin sojin na Iran inda ya ce abu ne mai wuya HKI ta kawo wa Iran hari, to amma idan har gigi ya debe ta yi hakan to za ta ji ba dadi daga dakarun na Iran.
Janar Firouz'abadi ya ce dakarun na kasar Iran suna ci gaba da sanya ido kan dukkanin wani motsi da makirce-makircen makiya Iran a kullum sannan kuma ba za su taba yin kasa a gwuiwa wajen sauke nauyin da ke wuyansu na kare kasar Iran da kuma juyin juya halin Musulunci na kasar ba.
1096600