IQNA

22:28 - September 14, 2012
Lambar Labari: 2411140

Ababe Masu Da Manzon Allah (SAW) Jan layi A Wurin Dukkanin Musulmi

Bangaren kasa da kasa, abubuwa masu alfama a cikin addinin muslunci da manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi suna matsyin jan layi ne a wurin dukkanin al’ummar musulmi kuma taba su zai jawo fushin duikkanin muslmi na duniya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-ahram, cewa wasu daga cikin manya akasar masar sun bayyana cewa abubuwa masu alfama a cikin addinin muslunci da manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi suna matsyin jan layi ne a wurin dukkanin al’ummar musulmi kuma taba su zai jawo fushin duikkanin muslmi na duniya baki daya.
Kafofin yada labarai na kasashen yammacin turai suna taka gagarumar rawa wajen karfafa gwiwar masu akidar cin zarafin musulmi da kuma keta alfarmar musulmi da addinin musulunci a duniya kamar dai yadda muke gani a duniya musamman ma a cikin nahiyar turai.
An watsa labarai masu karo da juna dangane da makomar majalisar ministocin kasar masar karkashin jagorancin fira minitsna Kamal Janzuri wanda masu tsaurin ra’yin kishin islama suke tuhumarsa da kasawa yayin da majalisar sojin kasar ba ta ba shi goyon bayn da yake bukata wajen gudanar da ayyukansa na tafiyar da mulki.
Mambobin majasar dokokin kasar Masar sun yi kira da a safke babban malamin kasar mai bayar da fatawa bayan ya yi tafiya zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da izinin majalisa da kuma yin shawara da majalisar malaman addinin muslunci ta kasar ba lamarin da ake kallonsa a matsayin wani babban kure. 1097568
captcha