Bangaren kasa da kasa, mataimakin shugaban kungiyar gwgwarmayar muslunci ta hizbullah a kasar Lebanon ya yi kakkausar suka dangane da shigar shigular da gungun 14 ga watan Maris na kasar ke yi a cikin harkokin kasar Syria musamman ma irin mummanr rawar da suke takawa wajen kara ruruta wutar rikicin kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar, cewa sheikh Naim Kasim mataimakin shugaban kungiyar gwgwarmayar muslunci ta hizbullah a kasar Lebanon ya yi kakkausar suka dangane da shigar shigular da gungun 14 ga watan Maris na kasar ke yi a cikin harkokin kasar Syria musamman ma irin mummanr rawar da suke takawa wajen kara ruruta wutar rikicin kasar ta hanyar aikewa da makamai da yan ta’adda.
Shi kuwa shugaban jam’iyyar Rasha demokradiyya ya sheda cewa bababr manufar taya da fitina acikin kasar Syria ita ce raunana kariyar da iran take da ita ta hanayawr kawancenta da gwamnatin Syria da suke baiwa gwagwarmayar palastinawa kariya da kuma ta Lebanon wanda ke bakantawa yammacin da karnukan farautarsu musamman ma daga cikin larabawa.
kungiyar alkaida ta ce ita ke da alhakin kai harin ta’addancin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da sukahada da fararen hula da jami’an tsaro a kasar Syria da sunan jihadi a tafarkin Allah kamar yadda kungiyar wadda ta shahara da irin wadannan ayuka ta sheda lamarin da ya fuskanci gagarumar suka da Allawadai daga al’ummomin duniya.
A nasa bangare dan majlaisar dokokin kasar Lebanon daga gugun ‘yan majalisa na kungiyar hizbullah Nawwaf Musavi ya yi kira da a warware matsalar kasar Syria ta hanyar lumana maimakon kara zuzuta wutar rikicin da ake gani yanzu haka daga wasu kasashen larabawa.
1097466