Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-ahram da ake bugawa abirnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar cewa, ana ci gaba da ba ta kashi tsakanin jami’an tsaro da kuma muslmi amsu zanga-zanga a kasar Masar a kusa da ofishin jakadancin kasar Amurka da ke birnin Alkahira domin kara tabbatar wa Amurka da cewa musulmi ba za su sake sanya ido sun kallon cin zarafin da ake wa addininsu ba ta hanayar wulakanta kur’ani mai a cikin makon nan.
Daya daga cikin membobin kungiyar 'yan jaridar kasashen larabawa a Amurka ya zargi wasu kasashen larabawa da na yammaci da kaddamar da gagarumin yakin jirkitar hakikanin abin da ke faruwa a kasar Siriya don cimma manufar da suka sa a gaba kan kasar.
A wata tattaunawa da ya yi da tashar talabijin din Press mai watsa shirye-shiryenta daga nan Tehran cikin harshen turanci, Rafik Lutf memba a kungiyar 'yan jaridar kasashen larabawa a Amurkan ya ce tashar talabijin din nan ta Amurka da Al-Jazeera ta kasar da sauran wasu tashohin kasashen larabawan su ne kan gaba wajen jirkita hakikanin abin da ke gudana a kasar Siriya da kuma zargin gwamnati da kashe fararen hula alhali hakan aiki ne na 'yan ta'addan da suke samun makamai daga wajen wadannan kasashen.
Har ila yau dan jaridar ya zargi tashohin da Aljazeera da watsa hotuna da faifai na bidiyo na karya kan abubuwan da ke faruwa a kasar Siriya. An jima dai ana zargin wadannan tashoshi musamman Al-Jazeera da shirya irin wadannan karararrki kan wasu kasashen larabawa da nufin cimma manufofin Amurka da na yahudawan sahyoniya.
1097390