IQNA

17:49 - September 16, 2012
Lambar Labari: 2412775

Tarayyar Turai Ta Bayyana Zanga-Zangar Da Ake Yi A Matasyin Hanyar Kara Tsatsauran Ra'ayi

Bangaren kasa da kasa, kungiyar tarrayar turai ta bayyana zanga-zangar da al'ummar musumi ke a koina cikin fadin duniya a matsayin wani abu da ake yin amfani das hi domin kara yawaita ayyuka na tsattasuran ra'ayin addini a cikin duniya da nuna kyama ga Amurkawa.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, kungiyar tarrayar turai ta bayyana zanga-zangar da al'ummar musumi ke a koina cikin fadin duniya a matsayin wani abu da ake yin amfani das hi domin kara yawaita ayyuka na tsattasuran ra'ayin addini a cikin duniya da nuna kyama ga Amurkawa sakamakon fitar da fim da aka yin a batunci ga manzon Allah.

A yau ma an ci gaba da zanga zangar nuna fushi da majigin nan wanda aka shirya a kasar Amurka mai nuna batanci ga addinin Musulunci a kasashen musulmi da dama.
An gudanar da irin wadannan zanga zanga a kasashen Lebanon Masar Yemen Sudan Tunisa da kuma Syria.

Gidan television na Press Tv mai watsa shirye shiryensa da harshen turanci a nan Tehran ya bayyana cewa an gudanar da zanga zanga a birnin Londan inda dubban musulmi suka nuna fushinsu da wannan majigin na matanci ga addinin mulunci wanda wasu yahuadawa suka shirya a kasar Amurka.

Masu zanga zanga a mafi yawan kasashen musulmi sukan kona tutucin Amurka da kuma HKI, a kasar Pakistan da kuma yankin Kashmir na kasar India ma an gudanar da irin wannan zanga zangar wanda ta yi Allah wadai da gwamnatin kasar Amurka da kuma wadanda suka tsara wannan majaigin.

Har’ila yau Dr Isma’il Salami wani masanin harkokin gabas ta tsakiya fadawa gidan television na Presstv cewa “yencin fadin albarkacin baki wanda kasashen yamma suke reyawa ba gaskiya bane, don yin wani abu wanda zai cutar da musulmi fiye da biliyon guda da raba a duniya ba yenci ba ne.

1098158






captcha