Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa ma'aikata harkokin wajen kasar Jamus ta fitar da wani bayani da a cikinsa ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da fim din cin zarafin manzon Allah da addinin muslunci wanda Amurkawa suka fitar tare da bayyana hakan da cewa ya sabawa dukaknin ka'idoji da dokoki na kasa da kasa da kuma kiyaye hakkin fadar albarkacin baki.
Ita kuwa majalisar kasashen larabawan yankin tekun fasha ta fitar da wani bayani da a cikinsa take yin Allawadai da kai farmakin da ake yi kan ofisoshin jaadancin Amurka a kasashen musulmi, bayan fitar da fim batunci ga manzon Allah da Amurka suka yi.
Majalisar mai mambobi kasashe 6, wato Kuwait, Bahrain, Saudiyya, Qatar, Oman da kuma hadaddiyar daular larabawa, sun fiar da bayanin ne domin nuna rashin jin dadinsu dangane da martanin da musulmi suke mayarwa a cikin fushi kan Amurka ta hanyar kai farmaki kan ofisoshin jakadancinta da ke cikin kasashen musulmi.
Dukkanin kasashen 6, wato Kuwait, Bahrain Saudiyya, Qatar, Oman da kuma UAE sun haramta gudanar da irin wannan zanga-zanga ta nuna kyama ga gwamnatin Amurka a cikin kasashensu, tare da yin barazanar daukar matakai masu tsanani kan duk wanda ya nemi yin wani gangami kan abin da yake faruwa.
1098198