IQNA

17:50 - September 16, 2012
Lambar Labari: 2412779

Fim Da Aka Fitar A Kasar Amurka Ba Shi Alaka Da Yancin Fadar Albarkacin Baki

Bangaren kasa da kasa, fim da aka fitar a kasar Amurka na cin zarafin addinin muslunci bas hi da wata alaka da abin da mahukuntan kasar suke rayawa nay ancin fadar albarkacin baki wannan wani mummunan aiki na cin zarafin al'ummar musulmi ta hanyar wulakanta m,anzon rahma.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Xin Hua, cewa shugaban kasar Tunisia ya bayyana cewa fim da aka fitar a kasar Amurka na cin zarafin addinin muslunci bas hi da wata alaka da abin da mahukuntan kasar suke rayawa nay ancin fadar albarkacin baki wannan wani mummunan aiki na cin zarafin al'ummar musulmi ta hanyar wulakanta m,anzon rahma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.

Sai kuma Majalisar kasashen larabawan yankin tekun fasha ta fitar da wani bayani da a cikinsa take yin Allawadai da kai farmakin da ake yi kan ofisoshin jaadancin Amurka a kasashen musulmi, bayan fitar da fim batunci ga manzon Allah da Amurka suka yi.

Majalisar mai mambobi kasashe 6, wato Kuwait, Bahrain, Saudiyya, Qatar, Oman da kuma hadaddiyar daular larabawa, sun fiar da bayanin ne domin nuna rashin jin dadinsu dangane da martanin da musulmi suke mayarwa a cikin fushi kan Amurka ta hanyar kai farmaki kan ofisoshin jakadancinta da ke cikin kasashen musulmi.

Dukkanin kasashen 6, wato Kuwait, Bahrain Saudiyya, Qatar, Oman da kuma UAE sun haramta gudanar da irin wannan zanga-zanga ta nuna kyama ga gwamnatin Amurka a cikin kasashensu, tare da yin barazanar daukar matakai masu tsanani kan duk wanda ya nemi yin wani gangami kan abin da yake faruwa a halin yanzu.

1098330


captcha