IQNA

Bangarorin Shri'a Na Ksashen Musulmi Su Dauki Matakai Kan Cin Zarafin Addini

14:52 - September 18, 2012
Lambar Labari: 2414464
Bangaren siyasa, ya kamata bangarorin shari'a na kasashen msuumi su dauki kwararn matakai na sharia'a domin shiga kafar wando daya da masu cin zarafin addinin mulunci a koina cikin fadin domin kawo karshen irin wannan wulakanci da ake gani.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa ya kamata bangarorin shari'a na kasashen msuumi su dauki kwararn matakai na sharia'a domin shiga kafar wando daya da masu cin zarafin addinin mulunci a koina cikin fadin domin kawo karshen irin wannan wulakanci da ake gani a kullum rana kan muslunci.

Majalisar dokokin kasar Yemen ta bukaci sojojin Amurka su fice daga babban birnin kasar Sanaa, mMajalisar ta bukaci ficewar sojojin ne bayan sanarwan da gwamnatin kasar Amurka ta bayar na cewa ta aike da sojojinta zuwa birnin Sanaa din bada kariya ga ofishin jakadancinta a can bayan zanga zangar da mutanen birnin suka yi a harabar ofishin a jiya jumma’a. inda suke nuna fushinsu kan majigin nan na batanci ga manzon Musulunci.

Yansanda a kasar ta yemen dai sun kama mutane da dama sun tsare kan zanga zangar nuna fushin da suka yi kan batanci ga Musulunci, har’ila yau an gudanar da zanga zangar nuna fushi ga majigi mai batanci ga Musulunci a birnin Sudney na kasar Australia a gaban ofishin jakadanci na kasar Amurca da ke can. Yan sanda sun kama mutane da dama wasu kuma sun ji rauni a lokacinda yansanda suka yi kokarin tarwatsa taron.

Hakama majalisar dokokin kasar Afganistan ta yi Allah wadai da majigin wanda yake muzanta manzon Allah (s), kuma ta bukaci kasar Amurka ta haramta majaigin ta kuma gurfanar da wadanda suke da hannun wajen yin sa.

1100701











captcha