Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Almanar, cewa mataimakin majalisar shawara ta hizbullah ya bayyana cewa gwamnatin Amurka tan afakewa da batun yancin fadar albarkacin baki wajen bayar da dama ga masu tsananin kiyayya da muslunci das u yi abin da suka ga daman a cin zarafin addini da wulakanci da sunan yancin fadar albarkacin baki kamar dai yadda kowayake gani a duniyarmu ta yau ba tare da wani shamaki ba.
A bangare guda kuma babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar daya daga cikin manufofin shirya fim din cin mutumcin Ma’aikin Allah (s.a.w.a) da aka shirya shi a Amurka ita ce haifar da fitina tsakanin musulmi da kirista a duniya sai dai kuma sakamakon nuna sanin ya kamatan dukkanin bangarorin biyu makiya ba su cimma wannan manufar ba.
Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar a daren jiya don yin allah wadai da wannan danyen aikin ya bukaci gwamnatin Amurka da ta dakatar da yada wanann fim din da kuma hana yada sauran abin da ya rage nasa da kuma daukan matakan da suka dace don ganin hakan ba ta sake faruwa ba, kamar yadda kuma yayi Allah wadai da halin ko in kulan da gwamnatin Amurkan take yi wa irin wannan cin mutumcin da ake yi wa Musulunci wanda ya ce shi ne ummul aba’isin din hare-haren da musulmi suke kai wa ofisoshi jakadancin Amurkan da kuma manufofinta a duniyar musulmi saboda ana ganinta a matsayin wacce ta yi tarayya cikin wannan danyen aikin.
Har ila yau shugaban na Hizbullah ya kirayi al’ummar musulmi da su ci gaba da nuna rashin amincewarsu da wannan danyen aiki don tabbatar wa makiya cewa a shirye suke su kare mutumcin Manzonsu komai rintsi komai tsanani, kamar yadda kuma ya kirayi gwamnatocin kasashen musulmi da su dau matakan da suka dace wajen tilastawa kasar Amurka, cibiyoyin kasa da kasa da kuma kasashen Turai wajen kafa dokokin da za su haramta cin mutumcin dukkanin saukakkun addinai na duniya da kuma annabawan Allah. 1100040