IQNA

Masu Adawa Da Muslunci A Canada Sun Gayyaci Ba’amurke Mai aadawa Da Musulunci

23:28 - September 25, 2012
Lambar Labari: 2419839
Bangaren kasa da kasa, masu tsananin adawa da addinin muslunci a kasar Canada sun aike da goron gayyata ga mutumin nan mai tsananin adawa da addinin muslunci na kasar Amurka wanda ya kone kur’ani mai tsarki kuma nuna fim din batunci ga manzon Allah tare da tozarta addinin muslunci.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na journal, cewa masu tsananin adawa da addinin muslunci a kasar Canada sun aike da goron gayyata ga mutumin nan mai tsananin adawa da addinin muslunci na kasar Amurka wanda ya kone kur’ani mai tsarki kuma nuna fim din batunci ga manzon Allah tare da tozarta addinin muslunci da mabiyansa.
A wani bayanin kuma cibiyar kula da ayyukan raya harkokin al’adu da na addinin muslunci a yankin palastine ta sanar cewa sojojin haramtacciyar kasar Isra’ia sun kai wani samame kan al’ummar yankin a cikin masallacin Qods mai alfarma a daren jiya a lokacin da ake gudanar da salla.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan ba shi ne karon farko da aka ga sojojin yahudawan sahyuniya suna kai irin wannan farmaki ba, lamarin da ya tunzura mutane da fusata su, amma dai ba biye musu ba wajen yin bata kashi ba.
Babbar cibiyar kula da ayyukan raya harkokin al’adu da na addinin muslunci a yankin palastine ta sanar cewa sojojin haramtacciyar kasar Isra’ia sun kai wani samame kan al’ummar yankin a cikin masallacin Qods mai alfarma a cikin makon jiya. 1105735
captcha