Bangaren kasa da kasa, babbar kotun jahar Saeo Batulo ta bai8wa shafin sadarwa na yanar gizo na youtube wa’adin kwanaki 10 da ya gaggauta cire fim din ann na batunci ga addinin muslunci idan kuma ba haka ba kotun za ta dauki tsatsauran mataki wannan shafi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa babbar kotun jahar Saeo Batulo ta bai8wa shafin sadarwa na yanar gizo na youtube wa’adin kwanaki 10 da ya gaggauta cire fim din ann na batunci ga addinin muslunci idan kuma ba haka ba kotun za ta dauki tsatsauran mataki wannan shafi wanda yake ci gaba da yada fim din.
A wani labarin kuma kasar Bahrain ta nuna maitar a fili tun daga lokacin da al’ummar kasar suka fara boren neman sauyi, da nufin tabbatar da adalci a tsakanin al’ummar kasar wadanda suke fuskantar zalunci da danniya tswon shekaru na tarihin kasar, amma abin da yafi komai ban mamaki shi ne yadda kasashen larabawa suka yi gum da bakunansu kan ta’asar da gwamnatin ta Bahrain take tafakawa.
Kalaman da Nabih Birri shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon ya yi a gaban baje kolin wasu hotuna da ke nuni da cin zarafin fararen hula da mahukuntan kasar Bahrain suke yi hakan ya harzuka sarakunan kama karya na kasar wadanda suke samun goyon baya daga sauran kawayensu ‘yan kama karya na tekun fasha da suka shahara da kama karya a tarinsu da masarautunsu.
1107647