Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na onislam, cewa a jiya wani malamin Addinin Kirista A kasar Swizerland ya yi kira ga shafin google da ya cire fim din batunci ga addinin muslunci tare da yin Allawadai da wannan fim tare da bayyana shi da cewa ya saba wa koyarwar addinin kirista da ma dukkanin koyarwar ta sauran addinai da ak asafkar daga sama kuma yin hakan batunci ga dukkanin addinai da aka safkar daga sama.
A ci gaba da zanga zangar nuna fushi da majigin batanci ga manzon Al…(s) da kuma zanen batanci da aka yi a kasashen Amurka da faransa, a farkon wannan watan, dubban daruruwan mutane a birane daban daban a kasar Pakistan a jiya Alhamis.
An gudanar da zanga zanga a birnin Multan a kudancin lardin Punjam a jiya Alhamis, masu zanga zangar sun bukaci gwamnatin kasar Pakistan ta kori jakadan Amurka da faransa daga kasar. Har’ila yau masu zanag zangar sun bukaci a hukunta wadanda suka samar da wannan majigin a kuma samar da dokoki na kasa da kasa wadanda suke hana keta hurumin addinan mutane.
An gudanar da irin wanna zanga zanga a biranin Islamabad babban birnin kasar da kuma yankin Baluchistan. Sai kuma birnin Quetta a kudu maso yammacin birnin karachi, da kuma birnin Karachi, da kuma Gujran-wala shi kuma a arewa masogabcin lardin Punjab.
1107941