Kamfanin dilalncin labaran iqnha ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadara na yanar gizolorient cewa, gwamnatin Turkiya ta rufe wasu shafuka da suke yada fim din batunci ga addinin muslunci wanda kasashen yammacin turai suka shirya da nufin bakanta sunan addinin muslunci a tsakanin al’ummominsu lamarin da ya fuskanci fushin mabiya addinin mulunci a koina acikin fadin duniya har da kasashen na turai.
Bayanin ya ci gaba da cewa adadin masallatai ya karu da kashi 74 cikin dari a kasar Amurka kamar dai yadda wani rahoto ya nuna wanda kungiyar jama’at Iman ta watsa a yau da ke cewa wannan adadi ya karu ne a cikin shekaru goma da suka gabata har zuwa karshen shekara ta 2011.
A cikin shekara ta 2000 masallatan da suke fadin kasar amurka a cikin dukkanin jahohi hamsin na kasar adadin bai wuce 1209 ba, amma ya zuwa shekara ta dubu biyu da goma sha daya adadin ya karu kashi saba’in da hudu idan aka kwatanta da wancan adadin, in da ya kai masallatai 2106 a cikin jahohi hamsin na kasar.
Wani bangare na wannan rahoto an yi ishara da cewa, mafi yawan matasa mabiya addinin muslunci mazauna kasar Amurka, sun yi amannar cewa manyan jami’an gwamnatin kasar suna tsananin gaba da addinin muslunci da koyarwarsa, amma hakan ba zai hana su ci gaba da gudanar da harkokinsu na muslunci ba.
1108660