IQNA

16:56 - October 03, 2012
Lambar Labari: 2425465

Hamas Ta Yi Barzanar Shiga Wani Sabon Boren Palastinawa A kan Sahyuniyawa

Bangaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmayar palastinawa ta Hamas ta yi barazanar cewa za ta shiga cikin wani sabon bore a dukkanin yankunan palalstinawa idan har hatamtacciyar kasar Isra'ila ta ci gaba da kai harin ta'addanci kan ala'ummar yankin zirin gaza.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam, cewa kungiyar gwagwarmayar palastinawa ta Hamas ta yi barazanar cewa za ta shiga cikin wani sabon bore a dukkanin yankunan palalstinawa idan har hatamtacciyar kasar Isra'ila ta ci gaba da kai harin ta'addanci kan ala'ummar yankin zirin gaza da sauran yankunan palstinawa.

A banagare guda kuma jagoran juyin juya halin Musulunci a nan Iran Aya. Sayyeed Aliyul Khaminaee, ya jaddada muhimmancin ranar Qudus ta duniya ga mutanen kasar Iran da kuma sauran al-ummar musulmin duniya. Jagoran ya bayyana haka ne a jiya lahadi a cikin khudubobinsa na sallar idi wacce a aka gudanar a masallacin jumma’a ta Jami’ar Tehran a nan birnin Tehran. Jagoran ya yaba da yadda aka gudanar da zanga zangar ranar ta Qudus a nan kasar Iran da kuma wasu kasashen duniya a ranar jumma’a da ta gabata, jumma’a ta karshe na watan Ramadan. Fiye da shekaru 30 da suka gabata ne Imam Khomaini (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya ayyana ranar jumma’a ta karshe na watan na Ramadan na ko wace shekara da ta zama ranar Qudus ta duniya, ranar da musulmi a nan kasar Iran da kuma sauran kasashen duniya zasu daga muryoyinsu da nunan goyinbayansu ga al-ummar kasar Palastinu wadanda ake zalanta. Jagoran juyin musuluncin ya kara da cewa, a cikin yan shekarun da suka gabata, kasashen yamma musamman Amurka da Ita HKI sun yi kokarin ganin sun mantar da al-ummar musulmi batun Palasdinu da kuma zaluncin da yahudawan Sahyoniyya suke musu, ta hanyar kokarin samar da sulhu, da kasashe biyu na al-ummu biyu ta Palasdinawa da kuma yahudawan sahyoniyya, Amma habakar da raya ranar Qudsu take samu a ko wace shekara da kuma borin farkawar Musulunci wanda ya taso koma ya ci gaba da faruwa a kasashen musulmi da dama a yankin gabas ta tsakiya, ya sake farfado da baton kasar Palasdinu, ya kuma maida shi matasala mafi muhimmanci ga al-ummar musulmin a duka fadin duniya. An gudanar da zanga zangar ranar Qudsu ta duniya ne a ranar jumma’a da ta gabata a cikin kasashen duniya kimani 70, inda musulmi masu azumi suka daga muryoyinsu suka yi ta kira da aka kawo karshen mamayar kasar Palasdinu suka kuma yi tir da manya manyan kasashen duniya masu goyawa yahudawan sahyoniyya baya kan mamayar da suke wa kasar Palasdinawa. A wani bangare na jamwabinsa jagoran juyin Musulunci, ya yaba da yadda sauran musulmi a wasu kasashen duniya suka kara shigowa don raya wannan rana, don ganin al-ummar Palasdinu sun fita cikin halin da suke ciki na zalunci.

1112204


































captcha