IQNA

HKI Na Ci Gaba Da Kisan Gilla Kan Al'ummar Gaza Da Suriya

11:14 - November 13, 2012
Lambar Labari: 2447495
Jiragen yakin h.k. Isra'ila suna ci gaba da kai hare-hare a kan yankin Gaza na palasdinu. A jiya litinin ma dai jirgin yakin h.k. Isra'ila ya kai hare-hare a yankin Gaza sai dai babu rahoton da ya ke nuni da asarar rayuka.


Wani shaidar ganin ido ya fadawa kamfanin dillancin labarun faransa cewa; jirgin yakin 'yan mamaya ya harba makami mai linzami akan wani wuri da babu komai a cikinsa a yammacin birnin Gaza abinda ya haddasa tashin gobara."
Har ila yau wani jirgin yakin ya kai hari akan wani fako da ke gabacin sansanin 'yan gudun hijira na Nusairat da ke tsakiyar Gaza.
A gabacin Gaza kuwa jiragen yakin h.k. Isra'ila sun rika yin shawagi akan sansanoni daban-daban na dakarun Izzuddin Qassam bangaren sojan kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas.
Tun a ranar asabar da ta gabata ce dai sojojin h.k. Isra'ila su ka tsananta kai hare-hare akan yankin Gaza wanda ya yi sanadin shahadar fiye da palasdinawa hudu.
Kungiyoyin gwagwarmayar palasdinawa sun maida martani ta hanyar harba makamai masu linzami a cikin h.k. Isra'ila tare da rusa motar soja guda da kuma jikkata sojoji biyar.




1136102

captcha