IQNA

12:49 - December 02, 2012
Lambar Labari: 2457078

An Bude Bankin Musulunci Ta Farko A Tanzaniya

Bangaren zamantakewa: a birnin darul Salam babban birnin kasar Tanazaniya an gudanar da wani gagaramin taro na bude bankin musulunci irinsa na farko a kasar da aka bawa taken Amana.




Kamfanin dillancin labarai Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a birnin darul Salam babban birnin kasar Tanazaniya an gudanar da wani gagaramin taro na bude bankin musulunci irinsa na farko a kasar da aka bawa taken Amana. A ranar juma'ar da ta gabata ce dai a hukumace mukaddashin ministan da ke kula da kasafin kudi da tattalin arziki na kasar ya jagoranci bukin kaddamar da wannan banki na musulunci a birnin Darul salama fadar mulkin kasar tanzaniyakuma an samu halartar manyan baki da masana da kuma ma'aikatan banki dam asana tattalin arziki na kasar kuma daga cikin wadanda suka gabatar da bayanai sun nuna gamsuwa da farin cikinsu da Allah ya nuna masu wannan rana da kuma irin alfanon da ke tattare da wannan banki da kuma sabon tsarin da ta kumsa .


1145912
captcha