IQNA

13:43 - December 10, 2012
Lambar Labari: 2461332

Hanyar Tabbatar Da Sulhu A Afganistan Ita Ce Ta Ficewar Sojojin Amerika da Wannan Kasa

Bangaren siyasa: Ramin mehman parast mai Magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran dangane da tabbatar da sulhu da tsaro a kasar Afganistan ya bayyana cewa;ficewar sojojin mamaye na kasashen waje da suka fito daga kungiyar tsaro ta Nato karkashin jagorancin Amerika it ace daya dayar hanya ta tabbatar da sulhu da tsaro a wannan kasa da kuma kawo karshen ta'addanci a wannan kasa.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da k eke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Ramin mehman parast mai Magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran dangane da tabbatar da sulhu da tsaro a kasar Afganistan ya bayyana cewa;ficewar sojojin mamaye na kasashen waje da suka fito daga kungiyar tsaro ta Nato karkashin jagorancin Amerika it ace daya dayar hanya ta tabbatar da sulhu da tsaro a wannan kasa da kuma kawo karshen ta'addanci a wannan kasa.A wani taron manema labarai da kakain ma'aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran ya yi a daren jiya a gaban manema labarai a birnin Karachi na kasar Pakistan dangane da ficewar sojojin Amerika daga kasar Afganistan a karshen shekara ta dubu biyu das ha hudu miladiya da kawo karshen mamaye wannan kasar ya kara da cewa:Amerika karkashin alkawalin da ta yi na yakar ta'addanci ta shigo yankin da kasar Afganistan amma yanzu wata hujja ce za su gabatar da za ta basu damar ci gaba da kasancewa a wannan kasa da nunuwa duniya don haka babu wani abu day a rage face ficewarsu daga kasar ta Afganistan.
1150127
captcha