IQNA

16:58 - December 18, 2012
Lambar Labari: 2466328

Musu Ziyara Akalla 17 Ne Suka Yi Shahada A Wasu hare-Haren Ta’addanci A Iraki

Bangaren kasa da kasa, akalla mutane 17 ne aka tabbatar da sun yi shahada a sakamakon hare-haren ta’addancin da aka kai a wasu sasas na kasar Iraki kan mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da suke gudanar da ayyukan ibada kamar dai yadda kafofin yada labarai na kasar suka tabbatar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo Ain cewa, mutane 17 ne aka tabbatar da sun yi shahada a sakamakon hare-haren ta’addancin da aka kai a wasu sasas na kasar Iraki kan mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da suke gudanar da ayyukan ibada a wurare masu tsarki.
Hare haren ta'addanci sun lashe rayukan mutane akalla 17 tare da jikkatan wasu fiye da 70 a sassa daban daban na kasar Irakai a jiya Lahadi. Majiyar tsaron kasar Iraki ta sanar da cewa Hare haren wuce gona da iri da aka kai sassa daban daban na kasar sun lashe rayukan Irakawa akalla 17 tare da raunata wasu 77 na daban, kuma hari mafi muni shi ne wadda a kai ta hanyar tada wasu motoci biyu da aka makare da bama bamai a wajen taron addini na mabiya shi'a a garin Karkuk da hakan ya lashe rayukan mutane 12 tare da jikkata wasu 57 na daban.
Har ila yau wasu 'yan ta'adda sun kai hari kan wajen binciken sojoji a yankin Addarimiyah, inda suka kashe sojoji biyu tare da jikkata wasu uku na daba. Kamar yadda fashewar wata mota da aka makare da bama bamai ta lashe rayukan mutane biyu tare da jikkata wasu 13 na daban a yankin Julula'I da ke yankin arewa maso gabashin birnin Bagadaza.
1155550



captcha