Bangaren kasa da kasa, masu tsananin adawa da addinin muslunci a kasar Amurka sun sake yunkurawa domin tsananta wannan gaba ga msulmin kasar da kuma duniya baki daya, musamman ma a cikin kasar wadda gwamnatinta ta kulla adawa da addinin muslunci da kuma yaki da shi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, yanzu haka dai masu tsananin adawa da addinin muslunci a kasar Amurka sun sake yunkurawa domin tsananta wannan gaba ga msulmin kasar da kuma duniya baki daya, musamman ma a cikin kasar wadda gwamnatinta ta kulla adawa da addinin muslunci da kuma yaki da shi a cikin kasar da sauran kasashe.
Wani labarin kuma yana cewa Wani bom mai karfi ya tashi a bakin ginin hukumar tsaron kasar Afghanistan a birnin Kabul. Kakakin ma'aikatar harkokin cikin gidan Afghanistan Sadiq Sadiqi wanda ya tabbatar da kai harin ya kara da cewa; bayan fashewar bom din an kuwa yi musayar wuta a wurare daban-daban na birnin Kabul.
Har ila yau, kakakin ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Afghanistan bai yi ishara da asarar rayuka ba kamar yadda wasu majiyoyin su ka yi. Bugu da kari wasu majiyoyin sun ce an ji karar fashewar wasu abubuwan masu yawan gaske a unguwar da ofisoshin jakadancin kasashen Amerika da Birtaniya su ke.
1171832