IQNA

Shugaban Majalisar Dokokin Iran Ya ce batunci Ga addinin Muslunci Aalama Ce Ta Gazawar Makiya

22:57 - January 17, 2013
Lambar Labari: 2481828
Bangaren kur'ani, shugaban majalisar dokokin kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa, irin matakin da makiya addinin muslunci suka dauka na yin batunci ga addinin muslunci hakan wata alama c eta nuna gazawarsu da kuma damuwa kan irin babban ci gaban da wannan addini yake samu.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a jiya shugaban majalisar dokokin kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa, irin matakin da makiya addinin muslunci suka dauka na yin batunci ga addinin muslunci hakan wata alama c eta nuna gazawarsu da kuma damuwa kan irin babban ci gaban da wannan addini yake samu a dukaknin sassa na duniya kamar dai yadda kowa yake sheadwa.

A wani rahoton na daban kuma jami’an tsaron kasar Iraki sun ce sun samu sa’ar kashae mayakan kungiyar Alkaida 10 a yau a yankin Anbar biyo bayan wasu hare-haren bama-bamai da mayakan na alkaida suka kai yau a sassa daban-daban na kasar Iraki.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a lardin Anbar Muhammad Khalaf Shalal ya bayyana cewa rundunar hadin gwiwa tsakanin sojoji da ‘yan sanda ta kaddamar da farmaki a wata maboyar mayakan kungiyar alkaida a yankin Hauran da ke cikin gundumar Anbar, yankin da ke makwaftaka da kasashen Syria da Jordan, wanda kuma ya zama wata hanya mafi sauki ga mayakan alkaida da ke shiga cikin Syria domin kai hare-hare daga kasar Iraki, kamar yadda wasu ‘ya’yan kungiyar daga wasu kasashen larabawa sukan zo Iraki domin shiga Syria ta wannan hanya.

Hare-haren da mayakan alkaida suka kai yau a kasar Iraki sun lashe rayukan fararen hula kimanin 24, yayin da wasu da dama suka samu raunuka, a jiya sun kai irin wadannan hare-haren a cikin birnin Bagadaza, wanda hakan yay a yi sanadiyar mutuwa fararen hula fiye da 30 da suka hada da kananan yara da mata. 1173103
captcha