IQNA

10:40 - January 31, 2013
Lambar Labari: 2488889

Kungiyar Kasashen Musulmi Ta Yi Allawadai Da Kone Wasu Littafan Musulunci A Tinbuktu

Bangaren kasa da kasa, kungiar kasashen musulmi ta yi kakkausar suka da yi Allawadai dangane da kone wasu daga cikin littafan addinin muslunci da wasu masu tsatsauran ra'ayi suka yi a garin Tinbuktu na kasar mali wanda 'yan tawaye suka kame shi a kwanakin baya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a cikin wani bayani da ta fitar kungiar kasashen musulmi ta yi kakkausar suka da yi Allawadai dangane da kone wasu daga cikin littafan addinin muslunci da wasu masu tsatsauran ra'ayi suka yi a garin Tinbuktu na kasar mali wanda 'yan tawaye suka kame shi a kwanakin bayaa arewacin kasar ta Mali.

A wani labarin kuma dangane day akin da ake yi a kasar Mali Kakakin rundunar sojin kasar Faransa da ke Mali ya sanar da cewa sojojin Faransa sun karbe iko da garin Kidal daya daga cikin manyan garuruwa uku da suke arewacin kasar ta Mali, wanda shi ne yan tawayen suka fara kwacewa a hannun azbinawa da suka fara daukar makamai.
Mai magana da yawun rundunar sojin Faransa da ke yaki a kasar Mali Thierry Burkhard ya bayyana cewar tun a cikin daren jiya sojojin Faransa suka kame babban filin jirgin saman garin Kidal, sannan da safiyar yau Laraba suka watsu a cikin garin domin farautar 'yan tawayen Mali, amma har ya zuwa yanzu babu wani fito na fito da sojojin na Faransa suka fuskanta daga mayakan 'yan tawayen.
Kame garin Kidal dai ya zo ne bayan kwanaki kadan da kwace garuruwan Gao da Timbuktu daga hannun 'yan tawayen Mali masu tsaurin ra'ayin addinin Islama, kuma wadannan garuruwa uku wato Kidal, Gao da Timbuktu sune manyan garuruwan da suke karkashin mamayar 'yan tawaye a yankunan da suke arewacin kasar ta Mali kafin fara kaddamar da hare haren soji kan kasar.
1180193



captcha