IQNA

23:20 - February 02, 2013
Lambar Labari: 2490031

'Yan salafiyya A kasar Tunisia Sun kai Farmaki kan wurare Masu Albarka a Kasar

Bangaren kasa da kasa, yan salafiya da suke bin tafarkin akidar wahabiyanci sun kai farmaki kan wurare masu albarka ada suke cikin kasar Tunisia kamar yadda suka ayi a yankunan kasar Mali da suka mamaye a watanni baya kafin dakarun kasar ta Mali da kasar faransa su fattatake su.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Afrik cewa yan salafiya da suke bin tafarkin akidar wahabiyanci sun kai farmaki kan wurare masu albarka ada suke cikin kasar Tunisia kamar yadda suka ayi a yankunan kasar Mali da suka mamaye a watanni baya kafin dakarun kasar ta Mali da kasar faransa su fattatake su da kwace ikon yankin daga hannunsu.

A wani labarin kuma Shugaban kasar Faransa Fransua Hollande ya jinjinawa sojojin kasarsa da suke yaki a kasar Mali, tare da bayyana cewa yana alfahari da su da kuma aikin da suke yi a kasar Mali, na yakar masu dauke da makamai da suka kwace iko da yankunan arewacin kasar Mali.

A lokacin da yake magana a gaban sojojin kasar da ke kasar Mali, shugaban na Faransa ya bayyana cewa, yana alfahari da su, domin kuwa sun dauki bababn hadari saboda 'yanto wata al'umma daga wasu mutane masu mummunan nufi, kuma Faransa ta yi hakan ne domin akrba kiran shugaban kasar Mali Diounkunda Traure, wanda ya nemi taimakon Faransa ta hanyar majalisar dinkin dinkin duniya, duk da cewa Faransa ta san hadarin da ke tattare da hakan, amma ta amince domin safke wannan nauyi.

A nasa bangaren shugaban kasar ta Mali Diounkunda Traure ya yi godiya ga shugaban kasar ta Faransa da kuma sojojinsa da suke yaki tare da sojojin Mali a arewain kasar domin abin da ya kira dawo da doka da oda a yankunan da masu kishin Islama da ke da alaka da alkaida suka mamaye.

Fransua Hollnade ya tafi birnin Tinbuktu, daya daga cikin muhimman biranan tarihi a nahiyar Afirka, wanda shi ma ya kasance karkashin ikon 'yan tawayen kafin sojojin Mali da na faransa su kore su, 'yan tawayen dai sun rusa dadaddun wuraren tarihi da dama da ke cikin birinin na Tinbuktu.

1181272

captcha