IQNA

12:59 - February 13, 2013
Lambar Labari: 2496038

Kira Ga Faduwar Gwamnatin Bahrain Shi Ne Take Na Karshe Da Al'ummar Kasar Za Su Bayar

Bangaren kasa da kasa, babban sakataren gamayyar jam'iyyn adawa akasar Bahrain da ke neman sauyi na demokradiyya ta hanyar lumana a kasar ya bayyana cewa taken karshe da al'ummar kasar za su bayar shi ne faduwa ga gwamnatin Bahrain matukar dai ta ci gaba da yin biris ga kiran da al'ummar kasar ke yi.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar talabijin din Lu'lua cewa, Abdulrauf Shaid babban sakataren gamayyar jam'iyyn adawa akasar Bahrain da ke neman sauyi na demokradiyya ta hanyar lumana a kasar ya bayyana cewa taken karshe da al'ummar kasar za su bayar shi ne faduwa ga gwamnatin Bahrain matukar dai ta ci gaba da yin biris ga kiran da al'ummar kasar ke yi da wannan bukata ta al'umma.

A bangare guda kuma wasu 'yan majalisar dokokin Birtaniya sun kakausar suka ga gwamnatin kasar dangane da yadda ta nuna halin ko in kula kan abin da suka kira cin zarafin 'yan adam da ake yi a kasashen Bahrain da kuma Saudiyya, saboda amfanin da Birtaniya take samu daga gwamnatocin wadannan kasashe.

Daya daga cikin 'yan majalisar kasar ta Birtaniya kuma mamba a kwamitin da ke kula batutuwa na kare hakkin bil adama na majalisar Lordat Eric ya bayyana cewa, gwamnatin Birtaniya tana yin harshen damo a cikin siyasarta dangane da batutuwa da suka shafi kare hakkin bil adama a duniya, inda ya ce Birtaniya tana sukar wasu kasashe kan cin zarafin dan adam, amma ba ta cewa uffan kan keta hurumin dan adam da mahukuntan Saudiyya da na Bahrain suke yi.

A nasa bangaren wani dan majalisar dokokin kasar ta Birtaniya Jermy Corban, ya bayyana cewa ba su gamsu da abin da gwamnatin kasar take yi ba na shiru da bakinta kan cin zarafin dan adam da ake yi a kasashen Saudiyya da Bahrain, kuma za su ci gaba da kalu balantarta har sai ta canja wannan salon siyasa da ya kira na munafunci.

Jami'an tsaron kasar sun tarwatsa masu Zanga-zangar da su ke kokarin isa dandalin lu'u-lu'a da ke tsakiyar birnin Manama. Jami'an tsaron sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma kulake da abubuwa masu kara domin tarwatsa masu zanga-zangar maza da mata da kuma kananan yara.

Zanga-zangar ta yau ta zo ne a matsayin share fage na babbar zanga-zangar da 'yan hamayyar siyasar kasar su ka kira domin tunawa da zagayowar lokacin fara neman kawo gyara ta fuskar siyasa a kasar.

A ranakun alhamis da juma'a ne za a yi gagarumar Zanga-zanga da kuma yajin aiki a duk fadin fadin kasar saboda tunawa da cika shekara biyu daidia da fara yunkurawar al'ummar kasar.

1188082










captcha