Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, masu Zanga-zangar sun jaddada cewa za su ci gaba da tafiya akan tafarkin shahidan da jami'an tsaro zuriyar ali khalifa masu mulki a kasar su ka kashe har zuwa cimma mafita. Jami'an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar nay au. Shekaru biyu kenan da al'ummar Bahrain su ka fara gudanar da gangami na zaman lafiya, wanda ya fuskanci murkushewa ta fsukoki da dama daga jami'an tsaron gidan sarautar kasar da kuma jami'an tsaron Saudiyya.
Mutanen biyu ne suka kai ga shahada a zagaye na farko na jerin gwanon lumana wanda mutanen kasar Bahrain suka fara a yau don cika shekaru biyu da fara juyin juya halin akasar. Wani matashi mai suna Hussain Al-jazaeri, da kuma wata yarinya mai suna Aminatu Mahdi duk sun rasa rayukansu ne sanadiyyar shakar hayaki mai sa hawaye wanda jami'an tsaron kasashen Bahrai da na saudia suka cilla kan gidajensu.
Har'ila yau jami'an tsaron na kasar Bahrain sun ci gaba da jefa hayaki mai sa hawaye a unguwannin daban daban a garuruwa daban daban na kasar ta Bahrain a yau Alhamis. Banda wannan wata majiya ta bayyana cewa gwamnatin kasar Bahrain ta rufe wani sashe na filin sauka da tashin jiragen sama na binin Manama a yau din.
Wasu kafafen yada labarain sun bayyana cewa jami'an tsaron kasar Bahrain din sun kama wakilin kamfanin dillancin labarai na Associated Press Mohammad Al-Sheikh, da Hassan Jamal na kamfanin AFP na kasar Fransa sai kuma Mazin Mahdi na kamfanin dillancin labaran DPA na kasar Jamus.
1193995